1 Oktoba 2014 - 15:59
Kasashen Iran Da China Sun Bayyana Rashin Gaskiyar Aniyar Amurka Ta Yaki Da Ta'addanci

Jamhuriyar Musulunci ta Iran da kasar China suna da tabbacin da’awar kasar Amurka kan yaki da ta’addanci babu gaskiya ciki.

A ganawarsa da manema labarai a yammacin jiya Talata; Ali Akbar Wulayati mai bada shawara kan harkokin siyasar kasa da kasa ga jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran ya bayyana cewa; Kasashen Iran da China suna tsananin kyamatar ayyukan ta’addanci kuma a shirye suke su yaki duk wani aikin ta’addanci, amma suna da tabbacin matakin da gwamnatin Amurka ta dauka na bangare guda wajen kai hare-hare ta sama kan kasashen Iraki da Siriya da sunan fada da ta’addanci babu gaskiya ciki.

Akbar Wulayati ya jaddada cewar yaki da ta’addanci dole ne ya kasance karkashin dokokin kasa da kasa. ABNA